Home LabaraiNajeriya ta aika rundunar sojoji 185 ƙasar Guinea Bissau domin wanzar da zaman lafiya

Najeriya ta aika rundunar sojoji 185 ƙasar Guinea Bissau domin wanzar da zaman lafiya

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Rundunar sojojin Najeriya ta kammala atisayen kai kwararrun sojoji 185 domin wanzar da zaman lafiya a kasar Guinea Bissau a ranar Juma’a.

Majiyar Dabo FM ta bayyana cewa sojojin sun fara atisayen ne a ranar 6 ga Junairu a Martin Luther Agwai International Leadership and Peace Keeping Centre (MLAILPKC), Jaji, dake jihar Kaduna a Najeriya.

A wani wakilci da shugaban sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya aike wanda kwamandan makarantar Nigeria Army School of Infantry (NASI), Kelvin Aligbe ya wakilta.

Buratai ya bayyana wannan yaye sojojin ya nuna sha’awa tare da gudunmawar da Najeriya take da ita na ganin an kawo zaman lafiya a fadin Duniya baki daya.

Daga karshe ya gargadi sojojin da cewa tsarin gamayyar kasashen yammaci Afirka, Ecowas baya yarda da cin zarafin mu’amala musamman ta saduwa.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00