Mon. Nov 18th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

‘Yar Najeriya mai shekaru 21 tayi fice bayan kammala karatun kiwon lafiya a kasar Turkiyya

1 min read

Yar Najeriya mai shekaru 21 da ta kammala karatun digirinta a fannin “Nursing” ungozoma tayi fice a cikin daliban kasashen waje da suka kammala karatun tare.

Maryam Ahmad Abdulhamid, yar asalin jihar Jigawa ta kammala karatun nata ne a jami’ar Near East University dake Nicosia, babban birnin kasar Cyprus wacce take makokantaka da kasar Turkiyya a tarayyar Turai.

Maryam mai shekara 21 ta kammala karatu da sakamakon kusan mafi kyawu a cikin kafatanin daliban makarantar inda tayi zarra a cikin daliban da suka kammala karatun ungozomanci.

Wakilinmu ya rawaito Maryam ta shafe shekaru 4 tana karatun inda a kowacce shekara ta kan samu sakamako mafi kyawu daga sauran dalibai abokan karatunta.

An dai haifi Maryam a shekarar 1998 a garin Malam Madori dake jihar Jigawa, jihar dake arewa maso yammacin Najeriya.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.