Labarai

Mudassir & Brothers ya rarraba tulin buhuhunan shinkafa a Kano

Kamfanin Mudasssir & Brothers dake da shedikwata a jihar Kano, ya rarraba buhuhhunan shinkafa masu tarin yawa a jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewar kamfanin ya rarraba shinkafa karamin buhu mai nauyin kilo 25 a unguwar Yalwa dake karamar hukumar Dala a birnin Kano kamar yadda wakilinmu ya ganewa idanuwansa a yau Alhamis.

DABO FM ta shaidawa idanuwanta yadda motar kamfanin na Mudassir & Brothers ta rika bi gida-gida tana rabawa mabukata da rana zuwa yammacin yau Alhamis tin daga karfe 1 na rana. Kafin daga bisani motar ta tsaya ana zuwa a karba, kamar yadda zaku gani a bidiyon kasa.

A zantawar wakilinmu da wanda ya jagoranci rabon shinkafar wanda ya bukaci mu sakaye sunanshi, ya bayyana cewar shugaban kamfanin, Alhaji Mudassir Idris Abubkar ne ya umarcesu da su rabawa mutane shinkafar.

“Alhaji Mudassir Idris Abubakar, shi ne ya bamu umarnin mu rabar da shinkafar nan, yace mu rabawa mutane har sai ta kare.”

“Tin jiya muke rabo, gashi yau munayi, gobe ma zamuyi har sai ta kare. A iya yau ma mun rabar da kusan buhu 1000.”

A nasu banagren, wadanda suka amfana da rabon shinkafar sun bayyana matukar jin dadinsu bisa ga tagomashin da suka samu.

Wani da muka zanta dashi, Auwal Abdulkadir Yahaya, ya bayyana jin dadinshi bisa ga shinkafar da ya samu tare da nuna godiyarshi ga kamfanin bisa abinda ya kira da aikin alheri.

Haka zalika yayi kira ga masu hannu da shuni da suyi koyi da irin aikin shugaban amfanin na Mudassir & Brothers, Alhaji Mudassir Abubakar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Dalibai sun hada N495,000 don jinyar d’an uwansu Dalibi

Rilwanu A. Shehu

Babu wadanda suke iya saka katin N100 a tallafin gwamnati – Minista

Dabo Online

Buhari ya bada kyautar magani, gidan sauro, kayyakin gwaje-gwaje da dala 500,000 ga kasar Malawi.

Dabo Online

Attajirar Najeriya ta bawa Najeriya tallafin Naira biliyan 1, zata rabawa Zaurawa da Marayu N25,000

Dabo Online

Bayan rahotan Dabo FM, wata gidauniya za ta kai dauki zuwa Makarantar Firamare ta garin Garo

Raihana Musa
UA-131299779-2