Mun bawa gwamnonin jihohi cikakken taimako – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kyautatawa gwamnoni jihar Kano.

Buhari ya bayyana haka ne a wata ziyara daya kai yau Alhamis a jihar Imo ta bude wasu ayyukan da gwamnan jihar , Rochas Okorocha yayi.

Rochas ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta tallafawa gwamnoni tare da cewa dukkanin gwamnoni zasu yi aiki tukuru idan sukayi amfani da kudin da gwamnatin take bayarwa ta hanyar daidai.

Ayyukan da Buhari ya jagoranci budewa sun hada da Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe, Sabuwar Shedikwatar ‘yan sanda da Asibitin Iyaye Mata da Yara duk a babban birinin jihar na Owerri.

Dabo FM ta tattaro cewa; Mataimakin shugaba Buhari, Yemi Osinbajo ne ya wakilcin shugaban.

“Da yake jawabi, shugaba Buhari yace “Gwamnatin tarayya dama dangin APC sune jinjina gareka. Daga cikin abinda ka cimma, zaiyu ace dukkanin gwamonin sun samarwa jihohinsu cigaba ba tare da neman dauki daga gwamnatin tarayya ba.”

“Gwamnatin tarayya ta baiwa gwamnoni dukkanin gudunmawa. Mun tallafawa jihohi kuma zamu cigaba da yin hakan.

%d bloggers like this: