Zan ruguje sabbin Masarautun jihar Kano – Abba ‘Gida-Gida’

Abba Kabir Yusuf “Gida Gida”, dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jami’iyyar PDP ya bayyana cewa zai rusha masarautu 4 da aka kirkira a jihar Kano “Idan ya samu nasara a Kotu.”

DaboFM ta tattara cewa Tin dai 8 ga watan Mayun 2019 ne, gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje, ya rattabawa dokar Karin maasarautu 4 a jihar Kano bayan da majalissar dokokin jihar ta kaddamar da dokar.

Mai magana da yawun dan takarar, Sanusi Dawakin Tofa ne yayi wannan kalamine inda yake rawaito abinda Abba Kabir Yusuf din ya fada akan Karin masarautun, Dawakin Tofa ya bayyana haka ne a wani bikin bude baki da akayi da kungiyoyin masu san’ar sufuri ta jihar Kano.

Abba Gida Gida ya bayyana Karin Sarakunan da gwamnatin tayi a matsayin wata sabuwar hanya ta kwashe kudin al’umma.

Ya kuma kakkausar suka zuwa ga gwamnan Kano bisa kora da hali da yayi wa Manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin jihar dama wadansu manyan malamai na jihar.

“A dai dai lokacin da yakamata mu fuskanci kalubalen da muke dashi na gyaren ababen cigaba kamar makarantu da asibitoci domin janyo cigaba, makiyan wannan jihar tamu kirkirar masarautu ne a gabansu domin su kwashe kudin al’umma.”

“Mun samu labara cewa Ganduje ya shirya kashe miliyoyin kudade wajen ginin fadar sabbin sarakuna tare da siyan manyan motoci na alfarma ga sabbin sarakan da ya nada a lokacin da ake samun talakawan gari da basa iya biya yaran su kudin makaranta.”

Majiyoyin DaboFM sun rawaito Abba Gida-Gida, ya kara da cewa;

“Muna so mu janyo hankalin Gwamna da cewa wadannan kudade da za’a kashe, za’a kasha su ne ba’a gurbin daya dace ba, akwai mutane sama da miliyan 3 da basa zuwa makaranta, akwai kusan matasa miliyan 4 da basuda ayyukan yi da kuma miliyoyin Almajirai suna yawo a kan titi suna rokar abinda zasu ci tare da rashin kyakkyawan wakilci.”

“Munyi sa’a wata babbar Kotu a jihar Kano ta rushe nadin sarautar da akayi, kuma na tabbatarwa mutanen jihar Kano cewa “Tarihi zai maimaita” kanshi idan muka samu nasara a Kotu.”

Majiyoyin DaboFM sun kara rawaito Abba Gida Gida yana cewa; “Zaman lafiya a tsakanin mutanen mu shine abinda yake gaban mu kullin; bazamu bari wani “Mahaukacin Zaki” da yake haushi da chizon duk abinda yazo hanyarshi ya sawalwaltar mana da tarihin mu na shekaru sama da dubu 1 ba.”

“Inaso inyi amfani da wannan damar wajen kira ga mutane da suyi amfani da wannan dama ta watan Ramadhan wajen yin addu’a dan samun nasarar mu a Kotu.”

Gargadi

Ba’a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta “submit@dabofm.com
%d bloggers like this: