Labarai

Gwamnatin jihar Kano na dab da kammala aikin wutar lantarki na Tiga

Aikin samar da tashar wutar lantarkin dai tin da fari gwamnatin da ta gabata ta Rabi’u Musa Kwankwaso ce ta fara aikin, gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta kusa kammala shi.

Inda yanzu aikin samar da wutar na Megawat 10 na Wutar ya kai kaso 90 cikin ɗari wajen kammala, in ji Injiniya Balarabe Shehu, ɗaya daga cikin injiniyoyi masu kula da aikin.

Mista Shehu, wanda shi ne Shugaban Kamfanin MBS Engineering, ya bayyana haka lokacin da Gwamna Ganduje ya kai ziyarar duba aikin a Tiga ranar Juma’a.

“Mun yi farin ciki da muka fahimci cewa wannan gwamnatin tana ci gaba da yin aikin da gaske da jajircewa.”

Ya kara da cewa “Control Room da Power Houses, da sauran su an kammala su 100 bisa ɗari. Muna fata ba zai ɗauke mu wata 2 ba zuwa 3 mu ƙaddamar da aikin.”

“Abinda ma zai sa aikin ya ɗauki wata biyu ko uku kafin a kammala shi ne shi ne akwai wasu abubuwa, musamman Dam ɗin Tiga da sai jihar ta nemi izini da cike-ciken takardu daga Gwamnatin Tarayya”, ya ƙara da haka.

A jawabinsa, Gwamna Ganduje ya tabbatar da shirin gwamnatinsa na neman izini daga Gwamnatin Tarayya a rahoton kafar yada labarai ta Labarai24.

“Muna kan tattaunawa da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Ƙasa. Saboda haka, kwanan nan wannan aiki zai kammala”, in ji Gwamna Ganduje.

Idan aka kammala aikin, in ji gwamnan, zai kula da buƙatun ɓangaren masana’antu a jihar.

“Jiharmu za ta dawo zuwa ƙarfin masana’antunta. Wannan Megawat 10, kamar yadda muka ambata zai kula da masana’antunmu da fitilun kan titi a cikin birni”, in ji Gwamna Ganduje.

Ya ƙara bayyana cewa ana yin irin wannan aiki a Dam ɗin Challawa.

“Buƙatarmu ita ce mu tabbatar da cewa an warware matsalar wutar lantarki, kuma zuba jari zai haɓaka a jihar nan. A sauƙaƙe, muna samar da kyakkyawan yanayin da kasuwanci zai farfaɗo.

“Sauran ƙananan sana’o’i ma za su farfado. Kuma zai taimaka gaya wajen magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin al’ummarmu”, in ji shi.

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin jihar Kano zata fara biyan albashin N30,000 a watan Disamba

Dabo Online

Kano: Cin Hanci: Ganduje ya rabawa wasu ma’aitakan INEC filaye

Dangalan Muhammad Aliyu

KANO: Ziyarar Atiku, alamar nasara ce?

Dangalan Muhammad Aliyu

Matasan Kano sunce Birin Gwaggo ne ya hadiye miliyan 7 a gidan namun dajin Kano – Kwankwaso

Dabo Online

Malaman Izala sun juya kalaman Kwankwaso don yayi bakin jini- Mal Aminu Daurawa

Dabo Online

Kotu ta sake dakatar da Ganduje akan kirkirar sabuwar Majalissar Sarkunan Kano

Dabo Online
UA-131299779-2