//
Thursday, April 2

Murna ta cika masu bautar Kasa bayan jin kararrawar alawus na N33,000

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Da ranar yau Juma’a, jami’an yiwa kasa hidima NYSC suja fara jin saukar alawus din su na Naira Dubu Talatin da Uku (33,000) da shugaba Buhari yayi alkawarin biyan su.

A satin nan da muke ciki ne dai, shugaban Hukumar ta kasa, Birgediya Shu’aibu ya bada tabbacin fara biyan sabon alawus jima wa ba.

Birgediya, ya tabbatar da hakan ne a wata ziyara da ya kai jihar Bauchi, in da ya tabbatar wa da jami’an cewa Hukumar ta shirya tsaf don fara biyan kudaden.

Wasu masu bautar kasar guda biyu a jihar Jigawa, sun shaidawa DABO FM yadda suka karbi sabon alawus din a yammacin yau tare da murna da yabawa shugaba Buhari bisa karin.

Masu Alaƙa  Kungiyar Kwadago ta bawa gwamnan jihar Niger wa'adin kwana 21 akan biyan albashin N30,000

Haka zalika sun bayyana jinjinarsu ga shugaba Buhari bisa cika alkawarin da ya dauka na biyan sabon alawus din.

DABO FM ta tattara cewar tin watan Afirilun 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan dokar mayar da albashin mafi karancin ma’aikacin Najeriya zuwa N30,000 daga N18,000.

Anyi ta tafka muhawar tare da zaman daidato tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya kafin fara biyan kudaden bayan watanni masu yawa.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020