Mutum 6 sun mutu a wajen wawusar abincin Korona a Taraba

Karatun minti 1

A kalla mutum 6 ne suka rasa ransu da dama suka jikkata a yayin da ake turmutsutsun wawusar kayan abincin tallafin Korona a garin Jalingo na jihar Taraba.

A jiya Asabar ne dai wasu da ake zargin bata-gari ne suka afka wa rumbum da gwamnatin jihar ta ajiye tallafin Korona, suka wawushe abincin dake ciki.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa Jaridar Punch cewar gawarwaki 6 aka mika zuwa dakin ajiyar gawa da safiyar yau Lahadi.

“Mun dauki a kalla gawa 6 zuwa Cibiyar Lafiya ta tarayya daga jiya zuwa wayewar garin yau.”

“Ana yunwa a Kasa, dubunnan mutane sun shigo domin su samu abincin, sai dai wasu sun mutu a kokarin hakan.”

“Wannan shi ne abinda gwamnati take so shiyasa taki raba wa mutane abincin.”

Zuwa yanzu dai gwamnati jihar Taraba ta sanya dokar ta-baci a garin na Jalingo.

Ita ma rundunar ‘Yan sandan jihar ba ta ce komai a kai ba.”

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog