Buhari ya bada kyautar magani, gidan sauro, kayyakin gwaje-gwaje da dala 500,000 ga kasar Malawi.

dakikun karantawa

Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sake bada kyautar kudi, dalar amurka 500,000 da kayayyakin gwaje-gwaje ga kasar Malawi.

Kayayyakin sun hada da magunguna da nauyinsu ya kai tan 30,000, maganin kwari, gidajen sauro mai dauke da sinadarin magani, Naira miliyan 180 da wadansu kayyakin kiwon lafiya da gwaje-gwaje.

Tawagar Ministan harkokin kasashen waje, Geoffery Onyeama, wadanda suka wakilci Najeriya, sun danka tallafin a hannun Ministan tsaro na cikin gida a kasar ta Malawi, Nicolas Dausi.

Da yake bada tallafi, Mr Geoffery, ya bayyana cewa; Najeriya zata cigaba da zama a matsayin ‘yar uwa ga kasahen Afrika tare da kin yin kasa a gwiwa wajen bada taimako ga duk kasar Afrikar da bukatuwar hakan ta taso.

“Muna jajenta muku akan abinda ya faru da kuma rashin da aka samu.”

“Iftila’in ya faru ne dai dai lokacin da muke gudanar da zabe a Najeriya, amma duk da haka shugaba Buhari ya umarcemu da hada wannan tallafin domin mu kawo shi cikin

“Mun iya hada kayayyakin lafiya 8000, injina da kayan gwaje-gwaje da kuma dalar Amurka 500,000.

“Kayayyakin suna da nauyin tan 30,000, wanda muke saka rai zasu iso muku nan da sati 2.”

“A yanzu tare damu akwai kadan daga cikin kayayyakin wanda muka turo a karamin jirgin domin wannan taron, sauran kuma akwai mai jigila C130 da zai kawo sauran.”

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ‘NAN’ ta rawaito cewa; a jawabin kasar ta Malami, baban Ministan tsaron cikin gida Nicolas ya bayyana jin dadinsu bisa tallafin da Najeriya ta basu.

“A madadin gwamnati da mutanen kasar Malawi hadi da wadanda iftila’in ya kora daga gidajen su, mutuna 886,000 da suka raunata, Inaso in gode muku kwarai da gaske bisa wannan jin kai da kuka nuna mana.”

Daga karshe sun taya shugaba Buhari murnar lashe zaben 2019 da yayi tin a watan Fabarairun daya gabata.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog