Labarai

N-Power: Gwamnatin tarayya ta dauki mutane 1,350 aiki a Ribas

Gwamnatin tarayya ta dauki mutum 1, 350 a jihar Kuros Ribas aikin kula da ayyukan noma a karkashin shirin nan na daukar aiki na wucin gadi wato N-Power.

Jaridar Leadership ta rawaito cewa Kodinetan Sasakawa Global 2000, na jihar, Ekok Ntua shi ne ya shaidawa manema labarai hakan jim kadan da kaddamar da shirin noman rogo a wata gona dake Okonde a karamar hukumar Ikom na jihar.

Ya tabbatar da cewa; an horas da matasa a karkashin shirin lura da ayyukan noma na N-Power, domin ganin sun lura da ma’aikatan da ke ayyukan noma a jihar. Ya ci gaba da cewa; Bankin duniya a lissafinsa ya ce; akalla a samar da mai lura da ayyukan noma mutum daya ga manoma 800 zuwa 1000. Inda ya ce; amma yanzu sai ka ga ma’aikacin dake lura da ayyukan noman daya yana kula da manoma akalla dubu 4.

Ya ce; horas da wadannan matasan zai taimakawa ayyukan noma a jihar, ta hanyar bunkasa kayayyakin noma da kuma ababen da ake nomawa da kuma fitar da su.