Kowin Lafiya

Maganin Kafso da aka hada da fatar Alade yafi inganci da aiki a jikin dan Adam – Bincike

Kwayar Kafso, nau’in sarrafa magani ne dake dangin ‘Solid Dosage Form’, ma’ana magunguna da aka cure a waje guda.

DABO FM tayi bincike domin sanin Kafso, amfaninshi da kuma yacce ake hada kwayar.

Bincikenmu ya tabbatar da cewa ana hada kwayar Kafso ne da sinadarin Gelatin, wanda shine kwanson da ake zuba ainahin sinadarin magani a ciki wanda ake kira da ‘API’.

Menene Sinadarin Gelatin?

Gelatin, wani sinadari ne mai dauke da sinadarin ‘Protein’ wanda ake samu daga fatar dabbobi.

Ana iya samun sinadarin Gelatin da nau’o’i 2;

  1. Mai dauke da ɓawo mai kwari. ‘Hard Shell.’
  2. Mai dauke da bawo mai laushi. ‘Soft Shell.’

Ya ake hada Sinadarin Gelatin?

Sinadarin Gelatin, ya rabu kashi 2 kamar haka;

  • Type A – Wanda ake samu daga fatar Alade.
  • Type B – Wanda ake samu daga kashushuwa da fatocin wasu Dabbobi.

Masana sun bayyana sinadarin Gelatin da ake samu daga fatar Alade yana da matukar kyan gaske bisa saurin narkewa da yakeyi da zarar an sha.

Zaku iya bayyana ra’ayoyinku a shafin na Facebook, Dabo FM.