Wani daga cikin tsofaffin mayakin kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ya bayyana farkon abinda ya fara jan ra’ayinsu suka shiga cikin kungiyar.
Tsohon mayaki da bai fadi sunanshi ba ya bayyana hakane ne a wata hirarshi da shashin Hausa na BBC.
DABO FM ta tattaro cewa; Ya bayyana cewa da Naira 3000 aka fara jan ra’ayinsu zuwa kungiyar ta Boko Haram bisa rashin aikin yi da yayi musu katutu.
“Kullin muna zaune a gida bamuda aikin yi, akwai daya a cikinmu, kullin yana fita yana dawo wa da dubu 5000, 6000 a hannu, yana mana siyayya”
Ya kara da cewa daga nan suka fara tambayarshi “in akwai wani abu da kakeyi muje muyi tare mana” inda ya ce; ya amsa musu cewar “Ku bari baza ku iya wannan ba.”
Hakan yasa ya fara jan hankalinsu ta inda ya bayyana cewa ya fara jan mutum daya a cikinsu, ya kaishi, “suka je sukayi suka dawo, daga nan ne ya bayyana cewa an fara bashi N3000.
“Muma muna zaune, suka same mu mukayi shawara, a haka suka ja ra’ayinmu.”
DABO FM ta tattaro cewa; tsohon dan Boko Haram din ya bayyana cewa; babu batun musulunci a aikin kungiyar, domin kuwa shima da farko, ya zata addinin akeyi wa aiki.
Inda ya bayyana cewa anayin Zina da matan da ake kamowa, shaye-shayen miyagun kwayoyi, wanda a cewarshi duk addinin musulunci bai yadda dasu ba.
Ya kuma kara yin tsokaci kan batun lamarin shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, inda ya bayyana cewa su ma da suke mayakan kungiyar a wancen lokaci, basu taba yin ido hudu da shugaban ba.
Har ma yayi togashiya da cewa “zancen Shekau fa kawai zance ne.”
Zamu cigaba da kawo muku hirar a nan gaba………………….
