ZabenKano: Kotu ta gayyaci Kwamishinan ‘Yan Sanda da hukumar INEC akan Shari’ar ‘Abba Gida-Gida’

Kotun sauraren korafe-korafen zaben gwamnan jihar Kano wacce ke da zama a kan titin Miller , Nassarawa, Kano, ta gayyaci Kwamishinan ‘Yan sanda domin bayyana a gabanta.

Kotun dai ta sake umarta INEC da ta bayyana a gabanta domin amsa tambayoyin da lauyan wadanda suka shigar da kara suka bukata. Sai dai kotun ta baiwa INEC zabi bayar da amsoshi a rubuce ba tare da zuwa ba.

A nasu bangaren, rundunar ‘yan sandan ta hannun wakilin Kwamishinan ‘yan sanda jihar Kano, Sunday Ekwe, ya bayyana cewa; “Kwamishinan yayi nisa a yanzu domin ya tafi wani muhimmin aiki.”

Mai shari’a Halima S. Muhammad ta karbi uzirin kwamishinan tare da bashi wa’adin kwanaki 5 domin ya dawo daga duk inda yake.

%d bloggers like this: