Na rantse bazamu sake satar kudin Najeriya ba – Atiku Abubakar

Karatun minti 1

Tsohon mataimaki kuma dan takarar shugaban kasar Najeriya karkashin inuwar jami’iyyar PDP yace bazasu sake satar kudi ba.

Atiku yayi wannan jawabi a gaban dubban masoya da suka fito yawo yakin neman zabenshi da yake zaga fadin Najeriya.

Kalamin da wasu magoya bayan shugaba Buhari suka ce, lallai ta tabbata Atiku ya saba dauke-dauke a baitul malin mutanen Najeriya.

Zaben Najeriya dai saura kwana 7, ‘yan takara sama da 38 sune ke neman shugabancin Najeriya a zaben da za’a gudanar a 16 ga watan Fabairun 2019.

Labarin da mujallar Najeriyar mu a yau ta wallafa, yaja hankulan mutane dayawa a kafafen sadarwa.

‘Yan Najeriya zasu yadda da furucin Atiku?

Zaku iya bayyana ra’ayoyinku a shafinmu na facebook da instagram.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog