(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

KANO: Ziyarar Atiku, alamar nasara ce?

dakikun karantawa

Jirgin yakin neman zaben shugubancin kasa na dan takarar jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, zai sauka a jihar Kano gobe Lahadi 10/02/2019, a filin wasa na Sani Abacha dake kwaryar birnin Kano.

Taron da aka dade ana dakun gudanar dashi tun bayan da shugaba Muhammadu Buhari yaje jihar Kano domin tallata kanshi don sake shugabantar kasar a karo na biyu.

Jihar Kano, jiya ce da take da dumbin tarihi wajen nuna kauna da soyayya ta shugaba Buhari, wanda bai taba rasa samun sakamako mai kyau a jihar ba tin farkon lokacin daya fara fitowa takarar shugabancin kasar.

Mutanen Kano zasu bada yardarsu ga Atiku?

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya samu wata sheda daga wajen mutanen Najeriya akan zargi na kasancewarshi ‘dan karbar rashawa da cin hanci a lokacin da suka shafe tsawon shekaru takwas suna jan ragamar mulkin kasar.

Wana tasiri Atiku yake dashi a idon al’ummar jihar Kano?

Mutanen Kano, mutane ne da suka waye wajen nemawa kansu mafita irinta siyasa, sai dai a batun zabin shugaban kasa, al’ummar Kano ana iya cewa masoyan Shugaba Muhammadu Buhari na hakiki domin kuwa basu taba yin rawa wajen kada masa kuri’arsu ba.

Sai dai bisa yacce alkaluma ke nuni da yacce wasu masanan siyasa  na ganin madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar, Engr Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso zai iya kawo wa Buhari cikas wajen samun nasara a jihar ta Kano.

Tafiyar Atiku da Kwankwaso zata iya raba shugaba Buhari da cin nasara jihar Kano?

Zaku iya bayyana ra’ayoyinku a shafinmu na sada zumunta, Dabo FM a facebook.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog