Naman Sallah hakkin Iyayen Samari ne – Martanin ‘Yan mata zuwa ga Samari

Samari dayawa sun koka kan yacce ‘yan mata a Sallar bana suka hana su naman Sallah.

Samarin sunce sam basuji dadin wannan matakin da ‘yan matan suka dauka ba.

DABO FM ta binciko cewa ‘yan matan sunce “Ramuwa mukayi”.

Hotuna da dama sunyi ta yawo a kafafen sadarwar musamman a bangwayen ‘yan mata a manhajar Whatsapp, inda suka alakanta bawa maza naman Sallar a matsayin hakkin Iyaye.

A wasu rubututtukan ma cewa suka yi “Duk saurayin da yace ki baci naman Sallah, kice masa ai hakkin Iyayenshi ne.

“Idan ya matsa miki, kice yazo ya karbi “Maggi” idan na gidan nasu ne babu dadi.”

Binciken DABO FM ya gano dalilin hana naman Sallar da ‘yan mata suka yi, yana da alaka da rashin yiwa ‘yan matan Kayan Sallah karama da suma Samarin sukayi ta cewa “Hakkin Iyayensu ne.”

%d bloggers like this: