Ni ba dan kwaya bane, ban ma taba sha ba – CP Wakili

Kwamishinan ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, CP Muhammad Wakili yace shi ba dan kwaye bane, hasali ma bai taba sha ba duk tsawon rayuwarshi.

A kwanakin bayan, mutane sunata cece-ku ce akan irin yadda kwamishan yake magana da kuma irin yanayin da yake shiga in yana magana.

Da yake magana da wakilin jaridar Daily Trust a ranar Asabar, Wakili yace a haka Allah ya halicce da murya da kuma yanayin magana irin na masu ta’ammali da kwayoyi.

“Watakila saboda dabi’u na shiyasa. Lokuta dayawa suna min kallon dan shaye-shaye. Ko idan ina magana da yanayin ban dariya, wasu na kallon wani abu sabo daga wajena. To ni dai a haka nake.”

“A haka Allah ya halicce ni, bazan iya chanzawa ba. Ni wasu miyagun magungunan ma ban taba jin sunansu ba sai da na zama ‘dan sanda.”

CP Wakili yace zai cigaba da bada gudunmawarshi wajen ganin an raba al’umma da ta’amalli da miyagun kwayoyi.

“Bazan zauna in zura ido a cigaba da wannan mummunar harka ba tare da nayi amfani da ‘yar damar da nake da ita wajen dakile abin ba.”

Daga karshe, Wakili yayi kira ga hukumomi musamman NDLEA, hukumar NAFDAC da hukumar shige da fice ta Kasa (Immigration) dasu kara kwaimi wajen ganin an kawar da dabi’ar shaye-shaye a ban kasa.

 

%d bloggers like this: