Zabe: Manya a jihar Kano, sun gargadi masu shiga hurumin siyasar Kano

Kwamitin Manya masu kishin jihar Kano, KCCI tayi gargadi ga wasu ‘yan siyasa dake shiga hurumin siyasar kasar Kano bayan kasancewar su ba ‘yan jihar ba.

Sun bayyana haka ne a wani taron manema labarai da Manyan jihar suka kirawo a yau Litinin 18/05/19, a birnin jihar ta Kano.

Shugaban Kwamitin, Alhaji Bashir Tofa yace kada wasu da ba ‘yan jihar Kano ba su zo su taimaka wajen kawo fitintinu a ban kasa.

A kwanakin baya, tin bayan da ake kasa da gudanar da zaben gwamnan jihar Kano, akaso samu rahotanni na wasu manyan wata jami’iyya sun shigo Kano domin duk yin duk mai yiwawa wajen tabbatarwa da tsagin wata jami’iyya nasara ko ta halin ka-ka.

Masu Alaƙa  Zaben Gwamna: Mataimakin Ganduje ya sha kayi a akwatin gidanshi

Rahotanni sunce akwai babban jigon jami’iyyar mai mulkin daga jihar Legas, shugaban jami’iyya da wasu tarin gwamnoni.

Kwamitin ‘yan kishin jihar Kano ya kara kira ga hukuma ta INEC data tabbatar an gudanar da sahihin zabe, kuma suyi kokari wajen tabbatarwa da duk wanda ya samu nasara nasararshi.

Daga karshe kwamitin yayi godiya ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano, karkashin kwamishan CP Wakili (Singham) bisa irin gudunmawa da hukumar ta bayar wajen bada cikakken tsaro a lokutan zaben shugaban kasa dana gwamna.

Sun kuma kara roko da rundunar ta kasance bata fifita wani bangare bisa wani bangare a zaben da za’a gudanar 23 ga watan Maris 2019.

Masu Alaƙa  Gwamnatin Kano nayin duk mai yiwuwa domin a chanza CP Wakili

Daga cikin manyan kwamitin akwai shehun malami, Sheikh Ibrahim Khalil Kano

Za dai a gudanar da zaben a rumfunan zabe 234 daga cikin kananan hukumomi 30 da za’a sake zabe a fadin jihar Kano.

 

 

Muhammad Aliyu Dangalan

•Sublime of Fagge's origin. •Apprentice Journalist. •Doctor of Pharmacy student.