Ko Sheikh Zakzaky zai warke a kasa da kwanaki 1416 da suka ragewa Buhari da El-Rufai?

Takaddama tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da shugaban IMN ta faro asali ne tin a shekarar 2015, a dai dai lokacin da gwamnati ta kama shugaban a matsayin alhakin tsare hanya da yan kungiyar ta IMN sukayi wa babban kwamandan sojojin Najeriya.

Hatsaniyar da ta haifar da asarar rayukan ya yan kungiyar ta IMN, biyo bayan rikice-rikice da dama wadanda suka biyo baya ciki har da zanga-zangar da mabiya kungiyar sukayi ta yi har na tsawon shekaru.

Daga bisani dai gwamnatin ta shigar da kara akan Sheikh Zakzaky bisa zargin aikata manyan laifuka wadanda suka hada da kisan kai da bautar da yara da wasu laifukan daban wadanda suka karya dokar kasa.

Masu Alaƙa  Gwamnatin Buhari zata samar da ayyukan yi miliyan 20 a zango na biyu - Minista

An dauki lokaci mai tsawo kafin shugaban IMN ya hallara a gaban Kotu domin fuskanta hukunci akan zarge-zargen da gwamnatin ta shigar a akanshi, lamarin da yayi sanadiyyar karuwar zanga-zanga daga yan Shia bisa ganin irin hali na rashin lafiya da malamin ya tsinci kanshi a ciki.

Daga nan ne lauyoyin shugaban na IMN, suka shigar da bukatuwar tafiyarshi kasar Indiya domin neman magani tare da matarshi wacce akayi awon gaba dasu tare da lokacin da jami an Sojoji sukayi wa gidansu dake garin Kaduna kawanya.

Ranar 5 ga watan Agusta, Kotu ta amince da bukatar Ak-Zakzaky na neman izinin fita kasar Indiya domin neman lafiyarshi, inda a ranar 13 ga watan Agusta, Malamin ya sauka a birnin New Delhi dake kasar Indiya.

Masu Alaƙa  El-Rufa'i zai kaddamar da shirin bada ilimi kyauta a Kaduna

A yanzu da DABO FM take tattara wannan bayanai, tini Mallam Zakzaky ya fara karbar agaji daga jami an lafiya a asibiti na kasar Indiya.

Sai dai manazarta na ganin cewa; “Sheikh Zakzaky bazai warke ba har sai shugaba Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Mallam El-Rufai sun sauka.”

Sauki da lafiya duk yana wajen Allah, amma a wannan karon masanan na nufin warkewa a takarda, wacce Likita zai rubuta masa ne cewa ya sallameshi.

Domin samun sauki daga matsin lambar da gwamnatin take yiwa babban malamin na Shia, ana ganin Malamin zai tsaya a asbitin har ya cinye lokacin da jagororin gwamnatin zasu sauka.

Wakilan DABO FM dake kasar Indiya sun tabbatar da cewa; Asibitin da aka Sheikh Zakzaky ya sauka a kasar ta Indiya, asibiti ne da yayi kauron suna a wajen yan Shiar kasar Indiya, domin dukkan yawancin manyan malaman Shia na kasar anan suke jinya.

Masu Alaƙa  Tsaro: Ka daina wasa da hankalin 'yan Najeriya -Kungiyoyin kare hakkin dan adam ga Buhari

Malamai irinsu, Moulana Kalbe Sahab Qibla wadanda suna daga cikin jagororin Shia a Indiya.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.