Valencia ta doke Barcelona a wasan karshe ‘Final’ na cin kofin Copa del Rey

Karatun minti 1

Kungiyar kwallon kafa ta Valencia ta lallasa Barcelona da ci biyu da nema a wasan karshen na cin kofin Copa del Rey da aka buga da yammacin yau Asabar 25/05/2019.

Valencia ta jefa kwallon farko ta hannun dan wasanta Kevin Gameiro a minti na ’12, inda Rodrigo ya kara jefa kwallo a ragar Barcelona cikin minti na ’33.

Barcelona ta samu farke kwallonta daya tal ta hannun dan wasa Lionel Messi a minti na 73.

Valencia ce ta lashe kofin na kakar wasan 2018/19 ta bana.

Alkalin wasa Alberto Undiano na kasar Spaniya ne ya busa wasan da aka buga a filin wasa na Estadio Benito Villamarin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog