Siyasa: Rigar 'Yanci

Rigar ‘Yanci: Sabon Salo , Gwamnan Jama’a da Gwamnan Shafaffu da Mai, Daga Dangalan Muhammad Aliyu

Zaku iya turo da naku sakon ta adreshin email dinmu a “submit@dabofm.com

Jihar Kanon Dabo, jiha mai abin mamaki, mai Dala da Goron Dutse, mai Gwamna biyu cikin zamani guda.

Kamar yadda kowa yasani, irin abubuwan da suka faru a jihar Kano kama daga farkon yakin neman zabe har zuwa kammala zabe.

Mun ga abubuwa masu ban mamaki, abubuwa na batan basira masu cike da abin kunya da takaici.

Munga abin kunyar da lamba daya ya janyo mana akan karbar rashawa, munji irin maganganu da Madugun Kwankwasiyya yayi akan wadansu malamai. Wanda duk muna fatan Allah ya gafarta kuma tare da yin afuwa ga mu baki daya.

Babban abin jan hankalin a yanzu shine, yadda gwamnatin Kano karkashin Dr Ganduje, tayi amfani da kassara harkar Ilimi da tayi wajen tara dandazon matasa marasa aikin yi da hangen nesa domin yin amfani dasu wajen tada fitintinu ciki kuwa harda ranar 23/03/19 da gwamnatin tayi amfani dasu wajen yin “tsiya-tsiya” domin komawa karagar mulkin Kano.

Sai gashi Allah cikin ikonshi, yau a jihar Kano an samu gwamnoni guda biyu, kamar yadda mutane dayawa ke fada.

“Gwamnan hukuma, shine gwamnan da hukumar zabe ta sanar a matsayin wanda lashe zabe, duk da cewa zaben bashida inganci.”

Sai dai fa tabar baya da kura, domin kuwa duk inda lamba dayan ya taka a cikin fadin Kano, jiya da ihu ne yake hadasu da mutan gari.

“Gwamnan kassara Ilimi, Gwamnan ‘Yan daba, Gwamnan ‘yan Drama, Gwamna mijin Goggo, Gwamna mai sinƘe, Gwamna mai kwadayin mulki.”

Daga daya bangaren kuwa, akwai Gwamnan Jama’a da kishin al’umma, Gwamna mai son gina rayuwar mutanen gari.

Allah cikin ikonshi duk inda ya taka, bata sauya zani ba, ji muke al’umma suna “Abba Gida-Gida”, “Mudai Abba muka zaba” “Abamu a huta”

Duba da jami’iyyar Abba Gida-Gida, na shirin mika kukanta zuwa kotu, al’ummar jihar Kano sun dade kuma basu daina mika kokon barar su wajen Jalla Allah ba, domin ya tabbatar da Abba a matsayin gwamnan Kano.

Karin Labarai

Masu Alaka

Rigar ‘Yanci: Abba Gida Gida ko Executive Mai Sinƙe?, Daga A.M. Fagge

Dabo Online

Zaben Kano: Tsaka mai Wuya ga Jami’iyya Mai Mulki, Daga Umar Aliyu Fagge

Dangalan Muhammad Aliyu

Zato Akan Buharin 2015: Nazata Buhari bazaiyi cuta ba, Daga IG Wala

Dabo Online

Ka nada Abdullahi Abbas sarkin Kano, hakan zai kara fito da irin tunanin ka, Daga Dangalan Muhammad Aliyu

Dabo Online
UA-131299779-2