(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Rigar ‘Yanci: Kwankwasiyya Farfagandiyya Limited, kashi na biyu Daga A.M.D

dakikun karantawa

Assalam Alaikum.

Ga masu bibiyar rubutu na akan mabiya darikar Kwankwasiyya da halayensu na ‘yada farfaganda, idan baku manta ba, nace ina zuwa da alakar ‘Yan Kwankwasiyya da Propaganda kashi na biyu, to yau Allah ya kawo mu.

Kafin in cigaba, zanso mika godiya ta ga hukumar gudanar wa “Dabo FM” duba da yadda suke bada damar karbar rubutun ra’ayi kowanne iri.

[irp posts=”5072″ name=”Kano: Alakar ‘Yan Kwankwasiyya da Propaganda, Daga A.M.D”]

A rubutun farko na fito da irin karai-rayin da ‘yan Kwankwasiyya suke yadawa, yanzu ma zan dora inshaa Allah.

1. Akwai maganar zuwa kotu da sukayi a baya, na cewa, yau Litinin, Kotu zata fara sauraron karar da suka shigar gabanta, wanda suke so a bawa Abba Gida-Gida mulki.

Kwatsam sai ga labari daga wajen manyan jami’iyyar PDP ya nuna cewa jami’iyyar bata ma shigar da kara gaban kowacce kotu ba balle a zauna yau Litinin, 1/04/19.

2. “Shugaba Buhari ya gayyaci Kwankwaso domin tattaunawa dashi a fadar gwamnati dake Villa a yau Litinin.”

Wannan ma na daga cikin farfagandar da mabiyan Kwankwasiyya sukayi ta yadawa a cikin wannan makon da muke ciki wanda labari ne da bashida gaskiya ballantana tushe domin babu magana daga bangaren gwamnatin shugaba Buhari.

 

3. Akan abubuwan da suka faru a lokacin gudanar da zaben cike gurbi a jihar Kano, tabbas maganar gaskiya, tinda munga abinda ya faru a jihar Kano.

A matsayina na dan jihar Kano, nasan an samu matsaloli na tada hankali a guraren zaben, sai dai ‘yan uwa na mabiya Kwankwasiyyar suna kambama abin gabaki daya. Akwai hotuna da suka rika sakawa wanda abin bama a jihar Kano ya faru ba.

Misali:

Wannan hoto bashida alaka da rikicin daya faru a jihar Kano, kamar yadda wata jaridar kasar Ghana ta bayyana.

3. Duk dai a kwanakin nan, ‘yan uwa ‘yan Kwankwasiyya sunyi ta kurari cewa suna da bidiyo, wanda ya nuna cewa gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje ya sa ambawa rundunar ‘yansanda, ma’aikatan INEC cin hanci domin su bari a murde zaben na Kano. Har ma sun rawaito adadin kudaden da duk baiwa wadanda na lissafa a sama.

Masu bibiyar ta, na barku lafiya, nan gaba zan kara zuwa da babi na 3.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog