(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Mutum 42 sun rasa rayukansu a harin da ‘Yan Bindiga suka kai wasu kauyukan jihar Zamfara

Karatun minti 1
"Yan BIndiga

‘Yan bindiga da ake zargi sun kai hari kauyukan Kware, Kurya da Kursasa da wasu makotan kauyukan karamar hukumar Shinkafi dake jihar Zamfara, harin da ya janyo rasa rayuka 42.

‘Yan bindigar sun shigo kauyukan tare da yin harbin mai uwa da wabi.

Shashin Hausa na BBC ya rawaito wata ganawa da wakilanta yayi da Sarkin Shanun Shinkafi, Dakta Sulaiman Shuaibu Shinkafi, ya shaidawa shaidawa BBC cewa, wannan al’amari ba wani sabon al’amari bane.

Dakta Sulaiman ya ce kimanin mutane 42 ne suka rasa rayukansu a lokacin harin da aka gudanar a kauyukan.

Ya koka kan yadda jami’an tsaro suke bada rashin kulawa da irin kashe-kashen da akeyi a yankin.

Daga bangaren Gwamnatin jihar Zamfara, ta hanyar mai magana da yawun gwamnatin, Mallam Ibrahim Dosara, ya bayyanawa BBC cewa mutane 28 ne suka rasa rayukansu a lokacin harin.

Itama rundunar ‘yan sandan Najeriya, shiyyar jihar Zamfara, ta hannun mai magana da yawun rundunar, Mohammed Shehu ya bayyanawa manewa labarai cewa iya mutum 10 ne suka rasa rayukansu a lokacin hare-haren.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog