Taskar Dabo: DABO FM ta nada sabon babban edita

dakikun karantawa
Albarkawa dabo fm

Hukumar gudanarwa ta kamfanin D.MAHSR Media Limited dake wallafa jaridar DABO FM, ta nada babban edita a sashin sabon sashin da ta bude na fitar da kwafin jarida ‘E-Newsapaper’ mai taken Taskar Dabo.

Jaridar da za ta rika fitowa a duk ranar Lahadin kowanne mako.

2036293-A-8598-4433-AB24-A300-DE202-D0-DMu’azu Abubakar Albarkawa ya fara aiki da DABO FM a matsayin babban wakilin jihar Kaduna. Ya rike shugaban riko na sashin al’amruan yau da kullin a DABO FM.

“Bisa kwazo da cancanta da samun horon aiki da ya samu wuraren aikinsa da suka hada da gidajen rediyoyin Alheri da Nagarta a Kaduna, shugabancin Albarkawa ya zama tamkar saka kwarya a gurbinta, in ji shugaban riko na D.Mahsr Media Limited, Muhammad Dangalan.

 

Karin Bayani a kan Mu’azu Abubakar Ahmad Albarkawa

Haifaffen garin Zaria dake jihar Kaduna, an haifeshi ranar 3 ga watan Nuwambar 1990, a unguwar Albarkawa jihar Kaduna. Ya yi karatun Firamare a Dr Shehu Idris Primary School Babban Dodo daga shekarar 1994 zuwa 2004, ya yi Sakandire a Sheikh Abubakar Gumi College duk a garin Zaria.

Ya yi Professional Diploma a bangaren Languages, National Diploma a bangaren aikin Jarida da kuma Diploma a bangaren Na’ura mai kwakwalwa a Nuhu Bamalli Polytechnic dake jihar Kaduna.

Yanzu haka ya na matsayin ‘Auditor General’ na kungiyar ‘yan Jaridu ta Najeriya sashin karamar hukumar Zaria, mukamin da ya fara a shekarar 2018.

Ya yi aiki a sashin Labarai na gidan Rediyon Nagarta ta jihar Kaduna da Gidan Rediyon Alheri a matsayin mai karanta Labara da mai gabatar da wasu shirye-shirye.

Ya rike matsayin baban edita a Jaridar Compass Times.

B64264-AF-B724-4-F56-94-A7-00862-ED9288-C

Karin Labarai

Sabbi daga Blog