BIncikeLabarai

Sarakuna 5, Hakimai 33 da Sojoji 10 keda hannu dumu-dumu a kashe-kashen Zamfara -Kwamatin Bincike

Kwamatin binciken kan kashe kashen jihar Zamfara a ranar Juma’a, ya kammala bincike inda ya gano hannu wasu masu mulkin gargajiya a kashe-kashen da suka faru a jihar.

Kwamitin ya tabbatar da cewa; a yanzu haka, suna da kwararan hujjoji wadanda suka tabbatar da hannun Sarakunan yanka 5 wajen hana zaman lafiya a cikin jihar.

Dabo FM ta tattara cewa rikicin na Zamfara, ya hallaka a kalla mutane sama da 6000.

Shugaban kwamitin kuma tsohon shugaban ‘Yan Sanda na kasa, Muhammed Abubakar, ya tabbatar da sa hannun Hakimai 33 wadanda yace suna hada hannu da ‘yan Bindigar wajen yin ta’asar.

Shugaban Kwamitin ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, dai dai lokacin da yake mika sakamakon binciken kwamiti ga gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle, a garin Gusau.

Ya kara da cewa sun samu hannun Sojoji 10 tare da wasu ‘Yan Sanda da ma’aikatan gwamnati a cikin kashe-kashen da ya gudana shekaru aru-aru a jihar Zamfara.

Shugaban Kwamitin ya kuma shaidawa gwamnan cewa; Binciken ya tabbatar da ya wani Sarki guda daya tilo tare da wasu Jami’an tsaro wadanda sukayi namijin kokari wajen dakile ta’asar da kuma kare mutane.