Sharhi kan maganar fin karfin Buhari da akayi akan rikicin Zamfara, Daga Yakubu Musa

Daga shafin Yakubu Musa a facebook, inda yayi sharhi da tambihi game da maganganun wani malamin addinin Islama a jihar Kano.

Yakubu Musa ya fara da cewa:

“Amma shi wannan Shehin malami da ban dariya yake. Ya ce mana shugaban kasa ya san wadannan manyan ‘yan Arewa da suke zub da jini a Zamfara, amma “abin ya fi karfin sa.”

Idan baku manta ba, jiya Sheikh ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinshi na Facebook, inda aka jiyo shi yana cewa yasan manyan da suke daukar nauyin kashe-kashen da ake yi a Zamfara, tare da nuni kan cewa al’amarin yafi karfin shugaba Muhammad Buhari.

Yakubu yayi martani da tambaya zuwa ga Sheikh na cewa Idan har yasan manyan arewa da suke a bayan kashe kashen, meyasa yace lokacin fadar sunansu baiyi ba? Yace “ko sai an gama kashe mu zai fada.?”

Masu Alaƙa  Yazamana dole 'yan siyasa sun girmama Sarakunan Gargajiya - Dr Pantami

Sheikh yace dalilan da yasa ake kashe kashen Zamfara da wanda akayi a Borno, ba wani abu bane illa dukiyar da akeso a sata wacce Allah ya ajiye a wadannan jihohi. “Borno saboda Man Fetur din dake dajin Sambisa”, Zamfara, saboda Gwal da wasu ma’adanai da ake sacewa.”

Martanin Yakubu Musa:

” Dan matikin da akai ya isa ya ga cewa kuma reason din da yabayar na ki san mutane a Zamfara ya sha bambam da na North East. Ya ce a Zamfara an tada hankali ne don kar mutane su ga ana ta hakar dukiyar nan ana fita da ita. Ana yi ne don dauke hankali. Sai kuma ya ce haka ne ma a yankunan Borno Saboda arzikin man fetir.

Masu Alaƙa  A guji yada jita-jita: Sheikh Dahiru Bauchi bai zagi Buhari akan rufe iyakoki ba

“Jama’a a tsaya a dan duba.  A zamfara ana hakar Gwal, a Borno kuma yaushe aka gano man ma da za a fara hakar? To wato suma ana ta kashe mutane ne a Borno dan kar’a ga man da manyan ‘yan arewa suke sata? Haba Malam!”

Da dukkan alamu, mutane dayawa na cewa, Sheikh ya kasance mai yada labaran yanar gizo-gizo ba tare da tabbatar da sahihancin su ba. Inda shima Yakubu ya ce ya tuna da wani maganin ciwon siga da Ya Sheikh ya taba bayarwa wanda ya gano a yanar gizo- gizo

Yakubu Musa: “Ko da yake ka taba bamu maganin diabetes ma ka ce mu sha kubewa ladies fingers za mu warke, kuma a Internet ka gani.”

Masu Alaƙa  Allah Ya’azurtani da samun ‘Ya’ya 70 da tarin Jikoki - Sheikh Dahiru Bauchi

Daga karshe, Yakubu, yayi jan hankali ga Malamai da su rika tantance abinda suka gani a yanar gizo gizo kafin su fadawa mutane, tare da fadar irin halin da mutum ka iya jefa kanshi idan aka cigaba a haka tare da misali.

“Kar fa mu manta haka wani malami ya ce an bawa Almustapha kwangilar kashe manyan Arewa. Da kyar ya kubuta da ga bulalar kazafi. Malamai ku ba da karatu amma ku tantance current affairs kafin ku fada. Wallahi ni ma da ba malami ba ba komai da na sani na ke gayawa jamaa ba.”

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.