Copyrighted.com Registered & Protected

Shugaba Buhari ya dakatar da hakar “Gwal” a jihar Zamfara

Jaridar Leadership Hausa ta rawaito:

A dalilin kara kaimi da gwamnatin Najeriya ta yi wajen ganin an kawo karshen ayyukan mahara da ‘yan ta’adda a garuruwan jihar Zamfara, sufeto janar din ‘yan sanda Mohammed Adamu ya bayyana cewa daga yau Lahadi gwamnati ta ba duk wani dan kasar waje dake hakon ma’adinai a jihar Zamfara ya tattara komatsan sa ya fice daga jihar.

Gwamnati ta ba duk wani dake da alaka da hakan awa 48 da su fice daga jihar ko kuma a kwace lasisin sa.

Bisa ga bayannan bincike da suka bayyana ga hukumomin tsaron kasarnan, an gano cewa atyukan hakan ma’adinai ne ainihin makasudin hayayyafa da tashe-tashen hankula da ake ta samu a jihar Zamfara din.

Masu Alaƙa  Shawarata ga Shugaba Buhari kan yadda za'a magance tsaron Borno da Zamfara, Daga Datti Assalafiy

Baya ga irin wannan tashin hankula, ayyukan ta’addanci da yin garkuwa da mutane sun zama ruwan dare a jihar.

Sannan an gano cewa su kan su masu hakon ma’adinan sune suka ruruta fitana a jihar inda rikici a tsakanin su da ramuwar gayya ke sa a na ta yawan samun fitinu a jihar da rashin zaman lafiya.

A dalilin haka tuni har an kaddamar da sabuyar shiri na yaki da mahara da masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara da Jihar Kaduna.

A ranar Asabar ne, sojojin Saman Najeriya masu yin sintirin Operation Diran Mikiya, sun samu nasarar ratattaka mahara masu dimbin yawa a wani babban sansanin su da ke Ajiya, cikin Karamar Hukumar Birnin Magaji, Jihar Zamfara.

Masu Alaƙa  'Yan Bindiga a Zamfara sun kashe shugaban 'Yan Banga

Daraktan Yada Labarai na Hukumar Sojojin Sama, Ibekunle Daramola ne ya bayyana a cikin wata takardar karin bayani da ya fitar ga manema labarai a Abuja.

Ya ce an kashe dozin da dama a dazukan cikin kauyukan Ajiya da Wonaka cikin Karamar Hukumar Birnin Magaji a Zamfara.

Masu alaka

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: