Labarai

Sojoji ne suka fatattaki ‘Yan Sandan da suka kama ni, suka sakeni na tsere – Dan Kidinafa

Rikakke kuma gagararren mai garkuwa da mutane, Hamisu Bala Wadume, ya bayyana yacce Sojoji suka taimashi ya tsere bayan da ‘yan sanda suka kamashi a garin Ibi na jihar Taraba.

Hamisu Wadume yace Sojoji ne suka taimakeshi ya tsere daga kamun farko wanda ‘yan sanda sukayi masa a jihar ta Taraba.

Idan baku manta ba a makon daya gabata ne, wasu Sojoji a jihar Taraba suka kashe ‘yan sanda 3. Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da jami’an nata sun kamo wani babban mai laifi ne a yayin da Sojojin suka bude musu wuta.

Shima a nashi bangaren, dan ta’adda Wadume ya bayyana cewa; Sojojin sun fatattaki ‘yan sandan da suka kamashi tare da tsinke magarkamin dake hannunshi, suka kuma saita shi a hanya domin tserewa.

A wani faifan Bidiyo da DABO FM ta binciko, wanda Abba Kyari, dan sanda mai kama masu manyan laifuka ya wallafa a shafinshi na Facebook, Hamisu Bala yayi bayani kamar haka;

“Nine Hamisu Bala, wanda yake da inkiyar Wadume. ‘Yan Sanda sukazo Ibi suka kamani, suna cikin tafiya dani sai Sojoji suka bisu, suka bude wuta har wasu ‘yan sanda suka rasa rayukansu.”

“Daga nan ne suka kaini Shedikwatarsu ta Sojoji, suka yankemin magarkamin dake hannu na, na gudu.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Yan Bindiga sun kone wani Matashi ‘Har Toka’ suka bawa iyayenshi akan sun kasa biyan kudin fansa

Dabo Online

Jami’in dan sanda ya rataye kanshi a bayan kanta

Dabo Online

‘Yan Bindiga sun yanka mai unguwa a jihar Sokoto, sun harbe ‘dan sanda 1

Dabo Online

Wani malami a babbar makaranta dake kano ya amsa laifin haike wa dalibarsa

Muhammad Isma’il Makama

Babu inda Boko Haram take da ko taku daya a Najeriya – APC

Muhammad Isma’il Makama

Jihar Edo: ‘Yan sanda sunyi arangama da masu sakawa mata yaji a al’aurarsu

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2