INA AMFANIN BADI BA RAI: Kuri’ata tafi Kudi

A cigaba da jan hankalin al’ummar Najeriya musamman mutane na arewaci akan siyarda ‘yancin da dokar kasa ta baiwa kowa.

Muna kara godiya ga Allah, daya sa muka ga zaben shugaban kasa dana ‘yan majalissun wakilai lafiya, batare da rasa rai ko wani mummunan tashin hankali ba.

Wane iri kalubale aka fuskanta a zaben daya gabata na shugaban kasa da ‘yan majalissar wakilai?

  1. Siyar da kuri’a

Duba da irin tangardar na’urar Card Reader da akayi ta samu, ya zamto mutane dayawa sunyi zabe ne kawai ba tare da tantancewar na’urar ba, ‘yan siyasa sunyi amfani da wannan dama wajen fito da kuri’u dayawa domin a rabawa mutane, tare da basu wani kudin da bai taka kara ya karya ba.

Masu Alaƙa  Kotu ta cire sunan Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na jami'iyyar PDP

A wani sharhi da aka gabatar a gidan Rediyo Freedom dake jihar Kano, an tattauna akan yadda aka rika siyan kuri’un mutane musamman mata akan kudi N150-500 a cikin birni, a karkara kuwa, wake da shinkafa ake kawowa wajen zabe a cikin farantin tafi da gidanka. Ya kai mai zabe, kasani cewa kudin da za’a baka bazai ishe ka kaci abincin kwana daya ba balle har kayi amfani da kudi wajen kashe wata matsala, ya kamata muyi aiki da lura wajen ganin mun kauracewa masu neman siyan ‘yancinmu.

2. Rashin sanin ‘yan takarkaru

Al’kaluma dayawa sun nuna wasu daga cikin al’umma basu ma san wadanda suke musu takara a matakan shugabancinsu ba. Anan ina ganin gazawar ‘yan siyasa na rashin bi ta lungu da sako domin tallata kansu ga masu kada kuri’a, tare da bayanna musu manufofinsu.

Masu Alaƙa  Zaben2019: Duk bakin cikin su sai na siyar da NNPC - Atiku Abubakar

Mafiya yawan lokaci ana yin zabe ne bisa sanin alamar jami’iyya ko wani dan takararta guda daya, wanda hakan na janyo zabar bara gurbi saboda guguwar soyayyar wannan mutum. Babban misali anan shine shugaba Muhammadu Buhari, dan dangwale na ganin kowa nagartattace ne kamar shi idan har sun tsaya takara a inuwar jami’iyya daya.

3. Rashin sanin yadda ake kada kuri’a

A zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar, bayan kiduddugar hukumar zabe ta INEC, an samu kuri’u sama da miliyan daya wadanda suka lalace bisa rashin bin ka’idar dan gwala kuri’ar, dangwalawa ba bisa ka’ida ba, ta hanyar dan gwalawa ba’a gidan a akeso mai kada kuri’ar zai dangwala ba.

Masu Alaƙa  Zaben2019: An kama kuri'a a gidan gwamnan Kogi, Yahaya Bello?

Hukumar wayar da kan al’umma ta Najeriya, ita ke da alhaki akan wannan, domin gwamnati na biyanta daga kudin al’umma domin a wayar musu da kai a kowanna fanni na rayuwa. Itama hukumar ta INEC tanada rawar da zata taka wajen shirya bitar koyawa mutane yadda ake kada kuri’ar musamman ga mutanen karkara.

Mun hadu a kashi na biyu.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.