Shirin mu akan zaben 2019 – ‘Yan Shi’a

Karatun minti 1

Kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Najeriya wacce aka fi sani da Shia, ta nesanta kanta daga wasu zarge-zarge da ake mata ciki hadda nuna goyon baya ga ‘dan takarar shugabanci kasa karkashin inuwar jami’iyyar APGA.

Dr Abdullahi Zango, daya daga cikin manyan kungiyar na kasa yace, babu wani shiri da suke na tada zaune tsaye a wajen zabe ko yi wani abu da zai kawo hargitsi a lokacin gudanar da zabe.

Kungiyar tace maganganun da wasu kafafen yada labarai suke fitarwa akansu, ba wani abu bane face karya.

“Bamuda wani shiri na kai hari ko ketare iyakar gidan kason da ake ajiye da ‘yan uwanmu da aka kama, wannan magana ba haka take ba”. Kowa yasan mu mutane ne masu neman zaman lafiya a koda yaushe, kuma ba’a taba jinmu da wani abu makamancin haka ba”

Ko a lokacin da shugabanmu, Sheikh Ibrahim Zakzaky yake nan, bamu taba nuna goyon bayanmu ga kowa ba duk ‘yayan kungiyarmu suna fita domin kada tasu kuri’ar.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog