Najeriya ta kafa tarihi wajen samun tsintsiyar da tafi kowacce tsintsiya girma a duniya.
A Lokacin da kasashen Africa suka tashi domin neman abubuwan cigaba da suka hada da gina hanyoyi, tashoshin jiragen kasa, gine-gine masu daukar hankalin bakin ketare da sauran kayan morewa rayuwa da cigaban kasa, ita kuwa Najeriya ta mike tsaye domin dasa tsintsiya mafi girma a fadin duniya.
Tsintsiyar da take a babbar kofar shiga garin Abuja, babban birnin kasar Najeriya ta ja hankalin masu amfanin da kafofin sada zumunta, inda kowa yake bayyana albarkacin bakinshi akan tsintsiyar.
Tambaya a nan itace, Anya tsintsiyar zatayi shara?
Bayyana ra’ayinka a shafinmu na sada zumunta a facebook da kuma instagram.