(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Shugaba Buhari ya amince da ginin sabuwar tashar jirgin ruwa a jihar Delta akan kudi dala biliyan 3.6

Karatun minti 1

Babban ministan harkokin sufuri, Mr Rotimi Amechi, yace gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari ta aminta da tsabar kudi dalar amurka biliyan 3.9 domin ginin gadar jirgin ruwa a garin Warri na jihar Delta.


Ministan ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya ‘NAN’ a ranar Talata a garin Abuja inda ya kara bayyanawa cewa gwamnatin ta aminta da ginin titin jirgin kasa daga gari har zuwa tashar jirgin ruwan.


“Shugaban Kasa ya bada kwantiragin tituna jirgin kasan Abuja zuwa Warri, Abuja zuwa Itakpe da kuma Itakpe zuwa Warri. Zamu gina sabuwar tashar jirgin ruwa a garin Warri akan kudin dala biliyan 3 da dugo 9.”


Ministan ya kara da cewa suna bukatar kashe dala biliyan 45 domin kammala dukkanin ayyukan titunan jirgin kasa a Najeriya.


Amechi yace da zarar an kammala aikin titunan jirgin kasan Lagos-Kano, Patakwal-Maiduguri, Lagos-Calabar da Abuja-Warri, kasar zata wadatu da jiragen kasa.


Ya kara bayyana cewa har ila yau, gwamnatin tarayya bata kasa sama da dala biliyan 3 ba wajen ayyukan titunan jiragen kasan da take yi.

“Aikin titin jirgin kasan Lagos-Ibadan ya cinye dala biliyan 1.6, banda kudaden da aka kashe na abubuwan da suka taso daga baya ba da kuma wanda bamu tsara ba. Abuja-Kaduna ya lukema dala biliyan 1.


“Mun kashe dala miliyan 500 wajen siyan kayayyakin aikin da durakun titin Lagos-Ibadan, bazan iya tuna nawa muka kashe a siyan irin kayan aikin a titin jirgin kasan Abuja-Kaduna.

NAN, DailyPost

Karin Labarai

Sabbi daga Blog