Akwai yiwuwar INEC ta soke zaben Zamfara bayan ganawar gaggawa da jami’iyyar APC tayi

Babbar hukumar zabe ta kasa, INEC ta yanke zata fitar da matsayar ta akan hukuncin da kotin koli ta fitar.

Hukumar tace; “Zamu zauna ranar Asabar 25/05/2019, domin tattaunawa akan hukuncin da kotu ta yanke tare da duban hukunci kuma zamu fadi matsayar mu a ranar Litinin 27/05/2019.

A ranar Juma’a ne babbar Kotun kasa ta yanke hukunci daya kwace zaben da jami’iyyar APC ta lashe a zabukan bisa tabbatar da rashin gudanar da zaben fidda gwani.

Kotun ta sanar da wadanda suke biye wa APC baya a yawan kuri’u, sune suka lashe zabubbukan. Sai dai a zaben gwamnan, jami’iyyar PDP zata iya samun kalubale.

Bincike DaboFM yace; Akwai yiwuwar hukumar zabe ta soke zaben ko mayar dashi wanda bai kammalu ba “Inconclusive” bisa dokar hukumar zabe da tace dole sai dan takara ya samu kuri’u na daya bisa hudu daga cikin biyu bisa uku na kananan hukumomin da suke jihar.

Majiyoyin DaboFM sun rawaito cewa a zaben gwamnan da aka gudanar a jihar, daga cikin kuri’u 810,782 da aka kada, jami’iyyar APC tana da kuri’u 534,541, PDP; 189,452.

Hakan ya nuna cewa PDP bata samu kason da zai iya bata kujerar gwamnan jihar Zamfara ba, dalilin yawan kuri’unta bai kai daya bisa hudu daga biyu bisa ukun kananan hukumomin jihar ba.

PDP tana bukatar samun jimillar kuri’u akalla 205,690 kafin lashe kujerar gwamnan jihar.

Suma a nasun bangaren, jami’iyyar APC ta shiga tattaunawar gaggawa a babbar shedikwatar ta dake babban birnin tarayyar Abuja bayan da Kotun kolin da yake hukunci.

%d bloggers like this: