Engr Saleh Mamman, Ministan lantarkin Najeriya.
Labarai

Tsakani da Allah har yanzu ba’a fara aikin Wutar Mambila ba – Ministan Lantarki

Sabon Ministan Lantarkin Najeriya, Sale Mamman, ya bayyana cewa maganar fara aikin Lantarki ta Mambilla, tatsuniya ce.

DABO FM ta tattaro cewa Ministan ya bayyana haka ne yayin wata ganawarshi da sashin Hausa na BBC.

Ministan ya kara da cewa; Rashin cimma matsaya tsakanin gwamnatin jihar Taraba da gwamnatin tarayya ne ya hana fara gudanar da aikin Lantarkin na Mambilla.

Sai dai ya bayyana cewa bayan kama aiki da yayi, kasancewarshi dan jihar kuma abokin gwamna, hakan ya bada damar gwamnatin jihar ta amince, an cimma matsaya domin fara gudanar da aikin.

Da yake amsa tambayar “Dama da ake ta maganar an fara aikin Lantarki, maganar tatsuniya ce kenan?”

Ministan ya shaida cewa; “Gaskiya, fisabillilahi, gaskiya guda daya ce, abin kamar da tatsuniya a ciki.”

Tin dai a shekarar 2017, gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari ta bayyana amincewa da bayar da kwangilar aikin Wutar Lantarkin Mambilla wanda zai kasancewa matattarar samun Lantarki mafi yawa a Najeriya.

Masu Alaka

To fa: Sanusi ya nemi Osinbajo yayi masa mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari bashi da lafiya

Muhammad Isma’il Makama

Bincike ya nuna “Duk dan Najeriya yana amfana da ‘Cin Hanci da Rashawa’ “

Dabo Online

Sabuwar taswirar kudin fasfo a Najeriya.

Dabo Online

Atiku, Kwankwaso, Tambuwal, Saraki, Lamido? PDP ta tsunduma neman dan takarar 2023

Dabo Online

Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 169.74 don gyaran tituna 10

Dabo Online

Da Dumi-Duminsa: Sabuwar Dokar CBN za ta fara aiki a yau Laraba

Rilwanu A. Shehu
UA-131299779-2