Shugaba Buhari zai bar Najeriya zuwa kasar Chadi a safiyar yau

Karatun minti 1

Shugaba Muhammad Buhari zai bar Najeriya zuwa kasar Chadi a safiyar yau Asabar, kamar yadda mai magana da yawunshi Mallam Garba Shehu ya fada.

Shugaba Buhari zai halarci taron kasashen “Sahel-Sahara” wanda ya kunshi kasashen 22.

Shugaban zai tashi yau Asabar, inda zai dawo da zarar an kammala taron a daren Yau.

Daga cikin wadanda suka raka shugaban sun hada da Gwamnan 3, na Lagos, Borno da jihar Osun.

Akwai Ministan cikin gida, Lt-Gen Abdurrahman Dambazau, ministan tsaro, Brig-Gen Mansur Dan Ali (Rtd), mai bawa shugaban shawar ta fannin tsaro, Major-Gen Muhammad Munguno, Shugaban hukumar shige da fice, Muhammad Babandede, da sauransu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog