0
Babban shugaban gudanarwar hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Sagir Madaki, ya rasu yau Talata a jihar Kano.
Kakakin hukumar, Sa’idu Muhammad Ibrahim ne ya shaidawa Jaridar Kano Focus.
Ya bayyana cewa mamacin ya mutu ne a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano da misalin karfe 4:45pm.
Zuwa yanzu an kammala jana’izar mamacin kamar yacce addinin Musulunci ya tanada a masallacin unguwar Yola ta jihar Kano, kamar yacce KANO FOCUS ta rawaito.
Marigayi Sagir Madaki, ya rasu yana da shekara 7, bar mata 1 da ‘ya’ya 7.
