Labarai

Sojin Najeriya sun gano wata makarkashiya da ake shiryawa a jihar Rivers

Shiyya ta 6 ta rundunar sojin Najeriya dake a garin Fatakwal, babban birnin jihar Rivers tace ta samu bayanan dake nuni da dauko hayar bata gari domin tada hargitsi a lokutan zabe.

“Wasu ‘yan siyasa sun debo wasu ‘yan bangar siyasa daga jihohi daban-daban na yankin Naija Dalta da nufin haifar da tashe-tashen hankula a ranar zabe.”

 

Rundunar ta bada tabbacin baiwa al’ummar yankin tsaro a kowana irin yanayi kuma a koda yaushe.

Gidan Rediyon Kano ya rawaito cewa, mai magana da yawun rundunar, Kanal Aminu Iliyasu shine ya bayyanawa manema labarai a wata sanarwa daya fitar daga ofishin sa.

“Mun gano an baiwa wasu ‘yan bangar siyasa makamai da kayan sawa na sojoji da zasu ringa bi rumfunan zabe domin tasa hankalin masu zabe.”

Yankin Niger Delta, yanki ne dake fama da rashin tsaro musamman a lokuta na zabe, wanda tarihi ya nuna kusan duk zabubbukan da suka gabata, ana samu salwantar rayuka a yankin.

 

Karin Labarai

Masu Alaka

Zaben Gwamnoni: Zan karɓi kayi idan na fadi zabe – Ganduje

Dangalan Muhammad Aliyu

KANO: Za’a sake zabe a akwatina 234 daga cikin kananan hukumomi 30 da aka soke -INEC

Dangalan Muhammad Aliyu

Kano: An shigar da kararraki 33 akan zaben Kano

Dangalan Muhammad Aliyu

Murnar Lashe Zaben Buhari: Matashin daya fara tattaki daga Kebbi zuwa Abuja domin taya Buhari murna

Na’urar tattara zabe ta INEC ta nuna Atiku ne ya lashe zaben 2019 – PDP

Dabo Online

Buhari yayi Allah wadai da dage zabe

Dabo Online
UA-131299779-2