Labarai

Akwai yiwuwar dasa abubuwan fashewa a guraren zabe, kasuwanni da guraren bauta – Masu Sa’idon Zabe

A cewar wasu masu saka ido akan zabe wadanda suka zo daga kasar Afrika ta Kudu, sunce akwai yiwuwar tashin bama-bamai a wajen zabe.

Mphoentle Keitseng, mai yada labaran hukumar, ya bayyanawa manema labarai a wani taro daya kira na kafafen yada labarai jiya a birnin Kano.

“Mun samu labarin wasu yiwuwar dasa abubuwan fashewa a wasu guraren zabe, Kasuwanni, Masallatai da Coci-coci.”

Mr Mphoentle yayi kira ga jami’a tsaro dasu dau damarar tsayar da yunkurin wannan harin.

“Muna kira ga gwamnatin Najeriya data kara kwakkwaran tsaro a wajen taruwar mutane, Masallatai da kuma Cocina.”

Saidai Mr Mphoentle yace jihar Kano bata daga cikin jihohin da za’a kawo harin kamar yadda ta samu labarin.

Da ake jin ta bakin rundunar yan sandan jihar Kano kuma, mai magana da yawun rundunar, DSP Haruna Abdullahi, yace basu samu wannan labari ba, kuma dama a shirye suke wajen tabbatar da zaman lafiya a lokutan zabe a fadin jihar Kano da kewaye.

 

Karin Labarai

Masu Alaka

Zaben Gwamna: Mataimakin Ganduje ya sha kayi a akwatin gidanshi

Dabo Online

#JusticeForKanoKids: ‘Yan sanda sun sake kubutar da Yaran Kano 2 daga Anambra

Muhammad Isma’il Makama

Ganduje, Sarki Sunusi sun jagorancin daurin auren Zaurawa 70

Dabo Online

Kano: Dole a fadi sakamakon zabe kafin sallar Isha – Kwamishina Wakili

Mahaifin Kakakin Majalissar Jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum ya rasu

Dabo Online

Anyi suya an manta da Albasa – Hon Kofa ya tashi a tutar babu

Dabo Online
UA-131299779-2