Siyasa

Kungiyar gamayyar kasashen turai, EU tayi Allah wadai da zaben gwamnoni

Hukumar gamayyar kasashen turai ta EU, tayi wadai da yadda hukumar INEC ta gudanar da zabubbukanta a Najeriya.

EU tace, Najeriya kasa ce mai kima a idanun duniya musamman a dimokradiyyance.

Shugabar jakadancin kungiyar, Maria Arena,  ta kara da cewa dole ne kasashe bazasu zubawa kasar ido ba, musamman idan akayi duba da irin abubuwan da suka faru a zabukan gwamnoni da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

“An samu kura-kurai da dama a zaben da aka gudanar, kama daga wajen kayan aikin hukumar zabe, yanayin tsaro dama yadda aka gudanar da yakin neman zabe.”

“Kimanin kusa mutum 600 ne suka rasa rayuwanku daga sanda aka fara gudanar da yakin neman zabe a watan Nuwambar 2018 zuwa yanzu da ake gudanar da zabubbukan.”

Shugabar da bayyana wadannan kalamai a taron manema labarai data kira a jiya Talata, a babban birnin tarayyar Abuja. – Reuters

Kama yanzu kasashe da dama sunyi tsokaci akan yadda zaben ya gudana, wadanda suke ganin zaben babu gaskiya a ciki.

Daga cikin kasashen akwai kasar Birtaniya, Morocco da kasar Congo.

 

Karin Labarai

Masu Alaka

Kano: An shigar da kararraki 33 akan zaben Kano

Dangalan Muhammad Aliyu

Satar akwatin zabe barazana ne ga rayuwa – Buhari

Dabo Online

Wallahi zan iya kashe mutum, in hakura da mahaifana akan Buhari – Matashi

Dabo Online

Kaduna: Hatsari ya ritsa da wasu matasa a wajen murnar cin zaben Shugaba Buhari

Dabo Online

Zabe2019: An kama ‘dan PDP da sakamakon zabe na bogi, a jihar Abia

Dabo Online

Kotu ta cire sunan Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na jami’iyyar PDP

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2