Tin ina yaro nake son taka leda a Real Madrid – Hazard

Dan wasa Eden Hazard, dan kasar Belgium, ya bayyana cewa yaso bugawa Real Madrid kwallo tin lokacin yana karami.

Dan wasan ya bayyana haka ne a wani sakon bakwananshi bari kungiyarshi ta Chelsea zuwa Real Madrid.

Hazard ya wallafa sakon a shafinanshi na sada zumunta, inda ya bayyana godiyarshi ga magoya bayan kungiyar da suka nuna masa goyon baya a tsawon shekaru 7-8 da yayi yana taka leda a kungiyar ta Chelsea.

Ya kuma godewa mahukunta da ma’aikatan kungiyar gaba ki daya.

Karanta cikakkiyar bayanin anan:

Masu Alaƙa  Magoya bayan Real Madrid sun yiwa Hazard ihun "Mu Mbappe muke so"

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.