Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Nayi rantsuwa da nufin isar da aikenku, zan sauke nauyinku da sahalewar Allah – Dr Shekarau

2 min read

Malam Ibrahim Shekarau, sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalissar dattijan Najeriya wanda aka rantsar ranar Talata.

Malam Shekarau ya bayyana haka ne jim kadan bayan rantsar dashi a matsayin sabon Sanata.

DABO FM ta tattaro cewa Shekarau ya gaji tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Kwankwaso a zauren majalissar.

“Cikin yardar Allah da ikonsa, yanzu aka rantsar dani a matsayin sanata da zai wakilci Kano Central a jam’iyyar APC. An rantsar dani tare da wasu takwarorina.”

“Yau ce ranar da na karbi amanarku, a matsayin wakilin bukatunku a majalisar dattijai ta Najeriya. Na amshi nauyin kananan hukumomi 15 na Kano Central.”

“Wannan rantsuwa ce da nayi domin Allah kuma cikin nufin Allah zan yi bakin kokarina na isar da duk aikenku. Zan sauke nauyinku da sauki da sahalewar Allah.”

“Ga jama’ar Kano Central da duk al’ummar Kano, ina sake yin godiya a gareku da nuna min kauna da yarda da kuka yi har Allah ya kawo mu wannan matsayin.”

“Da bazarku muke rawa. Don Allah ku ci gaba da yi mana addu’a da shawari nagari don samun dacewa a yau da gobenmu.” – Inji Malam Shekarau, kamar yadda majiyoyin DABO FM suka tabbatar.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.