//
Friday, April 3

Tukunna: Atiku bai shiga hannun mu ba kan badakalar biliyan 75.3 -EFCC

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Efcc ta bayyana labarin dake yawo a kafafen sadarwa kan batun ta damke tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jamiyyar PDP a zaben shugabancin kasa daya gabata, Atiku Abubakar a matsayin labarin kanzon kurege.

Rahoton Dabo FM ya bayyana labarin dai ya yadu kan cewa hukumar ta tsare Atiku tare da maka shi gaban Majistire Mojisola Dada ta kotun kebattattun laifuka dake Ikeja, Lagos.

Mai rikon shugaban yada labarai na Efcc, Tony Orilade shine ya bayyana hakan, ya kuma ce babu wannan magana ta tsare Atiku kan badakalar biliyan 75.3. Kamar yadda DailyNigerian ta wallafa.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020