Siyasa

Zuwan Hanan Buhari daukar hoto Bauchi cikin jirgin saman Shugaban Kasa ya yamutsa hazo

Zuwan Hanan a jirgin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani. Mutane da yawa sun kushe al’amarin domin anyi amfani da jirgin sama ne na sojin saman Najeriya don biyan bukatar ta.

A ranar Alhamis ne autar Buhari, Hanan Buhari tayi dirar mikiya a jihar Bauchi don halartar wani hawan daba na musamman a fadar sarkin Bauchi. Hanan ta isa jihar Bauchi ne a jirgin shugaban kasa.

Jaridar Hausa Legit.ng ta ruwaito cewa Hanan Buhari kwararriyar mai daukar hoto ce wacce ta kammala digirinta a fannin daukar hoto daga wata jami’a a London. Hakazalika, Hanan ta fita ta sakamako na ajin farko a fannin da ta karanta na daukar hoton.

Kwararriyar mai daukar hoton ta sauka ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi a ranar Alhamis. Ta samu tarba ne daga uwargidan gwamnan jihar Bauchi da sauran manyan jami’an gwamnatin jihar.

An gano cewa an shirya hawan daban ne don autar shugaban kasan ta samu damar daukar hawan, gine-ginen gargajiya da kuma sauran wuraren al’adu na jihar.

A matsayinta na kwararriya a fannin daukar hoton, Hanan zata hada hotunan ne don samun kundi guda na al’adu, hawa da gine-ginen masarautar jihar Bauchi.

Masu Alaka

Na dora yarda ta gareku – Buhari ya fadawa sabbin Ministoci

Dabo Online

Mun bawa gwamnonin jihohi cikakken taimako – Buhari

Dabo Online

Ra’ayoyi: Buhari a dafa su, Ganduje a soya su – Matashi

Dabo Online

Babu wani ci gaba da Buhari ya samu a yaki da Boko Haram -Kungiyar Tarayyar Turai

Muhammad Isma’il Makama

Ramadan: Buhari yayi kira da a cigaba da wanzar da zaman lafiya, soyayya tsakanin al’umma

Dabo Online

Mun bar barayi da Allah – Buhari

Dabo Online
UA-131299779-2