Turmutsutsu ya hallaka ‘Yan Shia 31, ya jikkata 100 a birnin Karbala na kasar Iraqi

Jamian Iraqi sun bayyana cewa; A kalla mutane 31 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani turmutsutsu daya faru yayin tattakin mabiya Shia a ranar Ashura da aka gudanar a birnin Karbala.

Mai magana da yawun Ministan Lafiya na kasar ya kara da cewa, mutane 100 ne suka jikkata tare da bada yiwuwar samun karin adadin wadanda suka rasa rayukan nasu.

BBC ta rawaito cewa; Turmutsutsun ya auku ne a dai dai lokacin da dubban mutane suka gudanar da tattakin.

Anayin tattakin ne domin tunawa da shahadar Sayyadi Hussaini, jikan Annabi Muhammadu, Tsira da amincin Allah su tabbata gareshi, wanda aka kashe a shekarar 680.

DABO FM ta tattaro cewa; Kowacce shekara, miliyoyin yan Shia ne suke zuwa birnin Karbala, wanda yake zuwa a ranar 10 ga watan Muharram. An tsayar da wannan rana a matsayin ranar bakin ciki da kuma tunawa da Sayyadi Hussain Rahimahullah.

Masu Alaƙa  Al-Zakzaki ya nemi kotu ta bashi izinin zuwa kasar Indiya domin duba lafiyarshi

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: