Haɗuwar Kwankwaso, Ganduje da tarin ‘yan majalissun Kano a Saudiyya

dakikun karantawa

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje da wasu muƙarrabansa da ƴan majalissun jiha da na tarayya na jihar Kano, su na ƙasar Saudiyya domin yin Umara a cikin wannan wata mai albarka.

DABO FM ta tabbatar da zuwan Hon Ali Baba Agama Lafiya Fagge, babban mai bawa gwamnan shawara kan sha’anin addinai, Hon Aminu Sulaiman Goro, ɗan majalissar tarayya mai wakilatar karamar hukumar Fagge.

Sauran sun hada da; Hon Kabiru Alhassan Rurum, ɗan majalissar tarayya mai wakiltar Rano da Hon. Ado Alhassan Doguwa, ɗan majalissar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Doguwa.

Shi ma ɗan majalissa mai wakiltar karamar hukumar birni, Hon Sha’aban Sharada ya ziyarci ƙasar.

Kazalika, DABO FM ta tattara cewa shi ma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso tare da tawagarsa sun isa ƙasar a yau Litinin, kamar yadda mataimakinsa kan watsa labarai, Saifullahi Muhammad ya bayyana.

A iya cewa wannan ba sabon abu bane na haɗuwar shugabannin Najeriyar a ƙasar Saudiyya musamman a lokutan ibada.

Sai dai wannan ƙaron abin zai ya shan bambam da yadda aka saba gani.

Har yanzu dai ana cigaba da  samun rikici a ƙungiyar Kwankwasiyya in da gidan siyasar ya tsage kashi biyu.

Daga cikin rikice-rikicen da su mamaye ƙungiyar akwai yadda wasu ke ganin a sake tsaida Engr Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda zai yi wa jami’iyyar PDP takarar gwamnan jihar a 2023.

Wasu kuma na ganin lokaci ya yi da ya kamata a sake ba wa wani dama, kamar yadda ƙungiyar ta saba canje-canjen ‘yan takarkaru.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog