Labarai

Zaria: Wanda ya cancanta kadai zamu bawa rumfa a kasuwar Sabon Gari – Musa

Yanzu haka dai an kaddamar da fara sayar da takardar mallakar sabbin rumfana na rukunin shagunan da gwamnatin Jihar Kaduna da hadin gwiwan wani kamfani za su gina a sabuwar kasuwar Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna.

Da yake kaddamar da fara shirin, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Alhaji Musa Mai Gwal, ya ce, bayan kammala dukkanin bayanai da aminta da yarjejeniyar da su ka yi da kamfanin, Sun amince membobin su musamman wanda rusau din kwanakin baya ya shafa, su mallaki rumfa a sabbin shagunan da za’a samar.

Ya kara da cewa, wannan wani bangare ne na cika alkawarin da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi, cewa babu wanda za’a ba rumfa a sabon kasuwar da za’a gina sai wanda aka rushe ma rumfa su a tsohuwar kasuwar.

Musa Mai Gwal, ya yi kira ga wanda za su amfana da shirin, su yi amfani da shi kamar yadda ya dace, kuma su yi kokarin cika ka’idojin da wannan kamfani ya gindayawa masu muradin mallakar rumfa a sabon kasuwar da za’a gina nan bada jimawa ba.

Da yake nashi jawabin, sakataren ‘yan kasuwar Alhaji Abbas Sardauna, ya ce, tuni shiri ya yi nisa domin tantance hakikanin ‘yan kasuwar domin gudun kada a yi kitso da kwarkwata, Wato a baiwa wasu na daban rumfuna a sabuwar kasuwar.
Ya kara tabbatar da cewa, ba za’a kammala aikin rijistan ba sai an tabbatar an kammala da dukkanin wadanda suka da ce a yi masu.

Wakilin kamfanin da za su gina kasuwar Alhaji Rabi’u Muhammad, ya ce, shagunan da za’a samar yanzu haka, sun bam-banta da wanda aka rushe ta fuskar girma da fadi, Kuma ya tabbatar da aniyar su na samarwa dukkanin wanda aka rushe ma rumfa sabon rumfa matukar yana bukata.

Idan dai za’a iya tunawa, a kwanakin baya ne gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin gwamna Nasiru El-rufa’i, ta rushe wani bangare na kasuwar Sabon Garin saboda sabuntawa, baya ga kasuwar Dan Magaji a karamar hukumar Zariya da kuma ta Kawo Kaduna a karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

UA-131299779-2