Home LabaraiDama can nasan Ganduje ne yaci zaben Kano -Buhari

Dama can nasan Ganduje ne yaci zaben Kano -Buhari

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya zababben Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje murnar nasarar da ya kara samu a kotin kare kukan ka.

Dabo FM ta tattara cewar sanarwar ta fito ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu a yammacin Litinin bayan yanke hukuncin da kotin koli tayi na jaddada nasara ga gwamna Ganduje da Simon Lalung gwamnan Filato.

Buhari yace “Ina cikin farin cikin hukuncin da kotu tayi a cikin alfarmar jam’iyyar mu, APC dama can ita ta lashe zabukan kuma ta kara tabbatar wa a kotu, ba karamin faduwa bace idan muka rasa jihohi kamar Kano da Filato.”

Ya kara da cewa ” A wajen yan adawa idan suka samu nasara to adalci kenan, idan kuma ta juye musu anan magana zata sauya.”

Tini dai akayi ta murnar a jihar Kano, bangaren yan hamayya kuma ana ta zaman makoki.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00