0
Sabon gwamnan Imo da kotin koli da damkawa kujerar gwamnan jihar, Hope Uzodinma ya bayyana zanga zangar da PDP keyi akan hukuncin kotun koli tana yi ne domin kifar da gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Majiyar Dabo FM ta bayyana sabon gwamnan yace “Idan maganar zaben da ya gudana a jihar Imo ne, me kuma zai kai masu zanga zangar hukuncin kotu har Abuja, Bayelsa da ko ina a fadin Najeriya.
“PDP tana so ne ta kifar da gwamnatin Buhari, zanyi amfani da wannan dama domi jan hankali ga jami’an tsaro domin yin bincike.”
Gwamna Uzodinma dai ya samu nasara daga kotun koli ne a cikin satin daya shude.
