Zamfara: ‘Yan Bindiga sun afka makarantar Sakandire ta ‘Yan Mata, sun sace mutane da dama

A wani hari mai kama da na ‘yan Boko Haram ranar Laraba, ‘Yan bindiga a jihar Zamfara sun kai hari wata makarantar ‘yan mata dake garin tare da sace wasu a cikin makarantar.


Sashin Hausa na BBC ya rawaito cewa ‘Yan bindigar sun afkawa makarantar Sakandire ta ‘Yan Mata dake Moriki, sukayi ta harbi kai mai uwa da wabi tare da yin awon gaba da mutane dayawa a cikin makarantar.


Majiyoyi sun bayyanawa BBC cewa maharan sun sace masu dafawa daliban abinci guda 4, Malamai 2, sai dai rahotannin su nuna maharan basu kai ga zuwa dakunan Daliban ba.

‘Yan bindigar sun tare dukkanin hanyoyin zuwa gari kafin su afkawa makarantar ‘yan Matan.

Masu Alaƙa  'Yan sandan Kano sun cafke mutane 100 da suka shiga jihar don fara ta'asar Garkuwa da Mutane


Ranar 14 ga watan Afirilun 2014 ne dai yan kungiyar Boko Haram suka sace daruruwan mata a makarantar ‘yan mata dake garin Chibok na jihar Borno

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.