(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');
/

Zaben2019: Ba abinda Buhari zai min, ko babu shi zanci zabe – Ganduje

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, yace zaben 2019 ko da Shugaba Buhari ko babu shi zai ci zaben shi.

A wata hira da gwamnan yayi a gidan radiyon Express dake birnin Kano, Ganduje yayin karin haske akan yadda magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari a jihar ta Kano irinsu Dan Balki Kwamanda, suke cewa gwamna Ganduje yana rawa ne da bazar shugaba Buhari ne kuma hakan ne kawai zai saka yaci zabe.

“Wannan kujera da nake kai ta gwamna, Buhari bai daga hannuna ba, kuma ranar zaben gwamnoni daban dana shugaban kasa ballantana ace zai taimakin wajen yin nasara, in Allah ya yarda zamuci zabe.” – Ganduje

Gwamna Ganduje na fuskantar kalubale dayawa daga wajen al’ummar Najeriya musamman mutanen jihar Kano tin bayan da faifayan bidiyon gwamnan suka fito na zargin karbar cin hanci daga wajen wasu ‘yan kwangila. “Bidiyon da jaridar Daily Nigerian ta wallafa”

A bari guda kuma, ‘Yan kwankwasiyya karkashin jagorancin Sanatan Kano ta tsakiya, Engr Rabi’u Kwankwaso na ganin gwamnan yayi musu butulci, wanda suma suke kokarin ganin sun sauke shi daga kan karagar mulkin jihar Kano.

Za’a gudanar da zaben gwamnoni a 9 ga watan Maris, 2019 biyo bayan dage zaben da hukumar INEC tayi a yau Asabar, daga 3 ga Maris zuwa 9 ga watan.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog